YAR AIKI COMPLETE
Title: YAR AIKI COMPLETE
Author: Ash24
Category: Other
Language: Hausa
Price: ₦ 500
No. of Words: 55555
Rating:
Your Rating:
Downloads: 10
Tags:
  • Hausa
  • Novels
  • Ash24
  • Soyayya

Description:
Khalid ne jingine jikin kofar da zata sadashi da falon mahaifinsa, Alhaji Abbas, yakai kusan mintuna biyar yana buga kofar falon cikin nutsuwa, ganin ba à bude kofar ba yasa shi jingina da jikin kofar. Aunty salma ce ta fito ta bude kofar falon, ganin khalid à tsaye jikin kofa shine yasata sakin fuska, cikin fara à ta bude masa kofar sosai yasa kai ya shiga. "yarona sannu da zuwa yau kaine da wuri Haka ? Ina kabar min surukata ? Cikin fara à take masa wadan nan tambayoyin. " ko zama banyi ba Aunty kike tsareni da tambayar ina surukarki, surukarki na gida, KO tashi batayi ba ma na fito ". Tab ! Kace ko sallama ba kayi mata ba ka fito ? Inafatan dai lfy ? " lafiya lau Aunty sammako nayo muku Alhaji nakesan gani kafin ya fita shiyasa nayo sammako dan ko gun Hajiya ban Shiga ba " Ai kuwa ka daki gurbi dan wallahi Alaji yayi sammako sunje gidan Alhaji Bukar, jiya cikin dare akayo masa waya yana gida ciwan ciki ya murdeshi cikin dare, toh Sun kaishi asibiti cikin daren Amma basu kwana ba suka koma gida, shine yayi sammako yaje yaga jikin nasa ". Ya Salam ! Aikuwa bari intashi inbisu inga jikin nasa. bari in leka mu gaisa da Hajiya sai in wuce daga nan. Aunty Natafi, cikin sauri ya tashi ya fice daga falon . kai tsaye bangaren mahaifiyarsa y dosa Hajiya jiddah, à gurguje suka gaisa ya fito ya doshi gidan Aminin mahaifinsa Alhaji Bukar dake unguwar farawa. Karfe goma Sha daya na safe agogon dake manne à babban dakin ya buga, bugawarsa yayi daidai da farkawar SUHAIMA daga baccin da ta kwanta tun jiya, idanuwanta ta daga takai dubanta kan agogo ganin da tayi lokaci ya ja, shine ta tashi cikin sauri ta fada bandakin dake makale à cikin dakin barcin maigidan ta. Wanka tayi, sannan ta sanya doguwar riga ta gabatar da sallar asubahi ,bata tsaya yin doguwar addua ba tafada dakin girki dan samun Abinda zata Sanyawa cikinta, sabida azababbiyar yunwar da takeji. Ruwan shayi ta tafasa ta sanya cikin fulas, ta soya wainar kwai ta debo kayan shayi ta nufi falonta dan ta karya kumallo. Kusan karfe d'aya na rana taji ana kwankwasa kofar falonta, Dan kwalli tayafa akanta, ta je domin ta bude kofar, tana budewa idanuwanta suka sauka kan aminiyarta, wata wawar runguma tayi mata suka shigo falon suna dariya. "kai kawata baki da kirki kiri kiri kinki zuwa gidana sai da à waya ko muyi chart " ? cikin dariya Nabila tace "Amma dai kya barni in zauna kafin ki fara yin mitar" yauma sa a kikaci nazo miki kema Ai ba kirkin gareki ba daga ke har khalid din. Wallahi kawata KO jiya mun dade muna hirarki. Hmm ! Ku kuka sani dai. Tashi ki samo min abinci yunwa nakeji. yunwa ? Aikuwa sai dai kisha shayi nima daxu shi na gama sha ,ko kuma ki shiga madafin ki dafa Ai kema nan gidanki ne kawata. Nabila kuwa kasake tayi tana kallanta, cikin mamaki, toh yanzu daga zuwa na gidan mutane ina bakuwa sai à tura ni kichin yin girki, wato Suhaima kiwar nan taki har yanzu baki daina ba duk fadan da akai miki bakiji ba ko !! "yanzu mijin nakima ruwan shayin kika bashi yasha da zai fita ? kinji ki ko da wani zance, idan baisha ruwan tea ba me zan bashi ? ni yauma ina bacci ya fita, Ban saniba ko ya karya ko bai karya ba ya fita. wani wawan kallo Nabila ta jefa mata, Amma kedai kin zama shashasha wallahi ace mijinka shine zai fita kana kwance kana baccin asara, ki tunafa ke amarya ce ko wata guda baku rufe ba,, baxaki tsaya ki kula da rayuwar mijinki ba, sai ki zama shasha cikin gidan Aurenki.
Share book:

Comments (0)